– Jaruma Maryam Yahaya ta bayyana cewa, rashin mijin aure ne ya saka har yanzu take yin harkar fim
– Ta ce komai lokaci ne da aure da mutuwa duka na Allah ne, saboda haka idan lokacinta yayi dole zata yi

– Ta bayyana irin nasarorin da ta samu a harkar ta fim da kuma wani babban kalubale da ta fuskanta a lokacin da take shirin fara harkar fim

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan wacce tauraruwar ta ke haskawa a yanzu, Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata yin aure a yanzu.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da gidan rediyon Freedom dake Kano, inda ta ce: “Aure da mutuwa duk lokaci ne na Allah, idan lokacina yayi zan yi dole, yanzu babu mijine, ku fito ku aure ni, rashin miji ne ya hanani yin aure, kowa yasan maza na wahala yanzu.”

Jarumar ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawan gaske a sana’ar da take yi ta wasan kwaikwayo, kuma ita babu abinda zata ce da wannan sana’a tata sai dai tayi godiya ga Allah.

Maryam ta bayyana wani babban kalubale da ta fuskanta, inda ta bayyana cewa da farko iyayenta sun ki amincewa ta shiga wasan Hausa fim din, yayin da ita kuma take matukar son shiga harkar.

Amma daga baya da fitaccen jarumin wasan Hausa Ali Nuhu yaje ya zauna da mahaifinta yayi masa bayani ya kyaleta akan taje ta fara wasan Hausan.

Kwanakin baya jarumar ta bayyana cewa tana matukar so taga ta fito a matsayin fitsararriya a fim, inda ta bayyana cewa ta fuskanci masoyanta suna matukar son su ganta a wannan fannin.

Source www.PressHausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here