A jiyane labarin cewa tauraruwar mawakiyar kasar Amurka, Nciky Minaj zata yi wasa a kasar Saudiyya ya bayyana inda dama, musamman musulmai sukai ta bayyana mabanbanta ra’ayoyinsu akan wannan lamari, itama tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bayyana ra’ayinta akai.

A sakon data fitar ta shafinta na Twitter, Maryam ta bayyana cewa, Salamu alaikum ‘yanuwa maza da mata ina da tambaya. Menene ra’ayinku akan wasan da Nicki Minaj zata yi a kasar Saudiyya? Ina son wakokinta amma bana goyon bayan wasan da zata yi a kasa me tsarki.

Download Sababbin Fina Finan Hausa A Nan Videos Films

Wasu dai sun bayyana cewa basu ga laifin hakan ba tunda ba a cikin garin makka ko Madina zata yi wasan ba.

Wasu kuwa sunce wasan na Nicki Minaj be dace ba.

Source www.PressHausa.Com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here