Connect with us

Kannywood News

An Yanka Ta Tashi:- Kutu Ta Janye Bada Belin Naziru Sarkin Waka


Wata kotu a jihar Kano ta tsare Naziru Ahmed Sarkin Wakar Sarkin Kano a gidan yari sakamakon rashin tantance wadanda za su tsaya masa.

Yanzu shahararren mawakin yana tsare ne a gidan yari na unguwar Goron Dutse da ke Kano.

Tun da fari dai kotun ta bayar da belinsa a ranar Alhamis bisa sharadin kawo wandada za su tsaya masa da tare da bayar da naira 500,000 da kuma kawowa kotu fasfonsa na fita kasashen ketare.

Gurfanar da fitaccen mawakin na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

Lauyan Nazir Ahmad Barista Sadik Sabo Kurawa ya shaida wa BBC cewar da zarar sun kammla matakan tantancewar zuwa gobe Juma’a za a saki wanda suke karewa.

Ana tuhumar Naziru ne kan wasu wakoki da ya yi kusan shekaru hudu da suka gabata.

Wakokin sun hada da Gidan Sarauta da Sai Hakuri.

An kama mawakin, wanda shi ne sarkin waka na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ranar Laraba da yamma.

Ranar Alhamis ne kotun ta bayar da belinsa bisa sharadin cewa zai bayar da fasfo dinsa da kuma samar da mutanen da zasu tsaya masa.

Mutanen sun hada da dagacin unguwar da yake zaune da ma’aikatan gwamnati biyu, kuma zai biya kudi ₦500,000.

Source www.PressLoaded.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending