Connect with us

Hausa Gist

Sako Zuwaga Dr Ali Isah Pantami Mai Zafi

SAKO ZUWA GA BABBAN MINISTAN SADARWA SHEIKH MALAM ISA ALI PANTAMI…

Da farko muna kara yabawa tare da jinjina maka akan yinkurin da kake na tsaftace hanyoyin sadarwa a bangaren kiran waya, da kuma daukar matakai akan su kamfanonin dake samar da layukan kira da Internet, umarnin kulle layuka sama da miliyan tara marasa rigista a Nigeria, babban abun a yaba ne…..

Sheikh Minista, muna kara kira daka sake bayar da umarni ga kamfanonin sadarwa akan su dakatar da rigistar layi da akeyi a wajen ofishohinsu, sannan duk wanda zai sayi sabon layi sai yazo da cikakkiyar shedar da zata tabbatar da cewa shine, idan so samu ne ya kasance Lambar BVN tana daga cikin ka’idojin yin rigistar sabon a Nigeria…..

Maigirma Minista muna kara kira daka duba tsarin nan da ake amfani dashi wajen boye Lamba a yayi kira, wasu yan Nigeria masu mugun nufi sukanyi amfani da hakan wajen kiran waya tare da boye lambarsu su aikata wasu laifukan, musammam a yanzu da aka kulle layuka marasa rigista, rahoto ya fara zuwa akan cewa Masu garkuwa da mutane suna boye lamba ne idan zasu kira iyalan wanda suka kame, Maigirma Minista akwai kasashe masu yawa a duniya da suke amfani da wannan tsarin na hana kiran waya da boyayyiyar lamba….

Sheikh Malam Pantami Minista muna fatan dai zaka sake bawa kamfanonin layuka umarnin saka tsarin GPS akan kowacce lambar dake Nigeria , duk masu layuka a Nigeria a sanya suyi Update din Rigistar da sukayi wajen saka Location akan layukan nasu, ta yadda duk lokacin da ake bukatar sanin wani bayani akan wani, zaayi amfani da bayanan nasa wajen bibiyar dukkan motsin da yayi, inda yake da guraren da yaje gaba daya…

Maigirma Minista muna cigaba dayi maka fatan alheri tare da samun nasara a wannan babban aikin dake gabanka.
Source www.Pressloaded.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending