Connect with us

Hausa Gist

Sirrin Rike Miji Garemu Mata

*SIRRIN RIKE MIJI*

Ina son mata ku tsaya fahimci yaya infection yake haifarwa mutane matsala sannan kuma ya dace ace kuna kula da yaranku da kuma ku kanku 

Ina son kusani cewa a wannan zamanin infection yana daya daga cikin abubuwan dake haifarwa mata da maza matsalolin da basu samun zaman lafiya a tsakanin ma aurata 

Wato abinda nake son ku gane anan shine kamar yanda babba ke kamuwa da infection haka ma yara za su iya ɗauka da sauri domin jikinsu ba shi da ƙwari nan da nan za su kamu da cuta, don haka idan uwa kina fama da infection ka da ki yi zaton yaranki ƴan shekara goma ko ƙasa da haka ba za su iya kamuwa da shi ba, akwai mata da yawa da suka zo mun da irin wannan problems na yara qanana suna da infection suna kuma azabtuwa. Don haka abubuwan da na ke fadawa manya haka ma yara za a iya basu. 

Ki rinqa ba su shayi mai citta, kanumfari, hulba kadan, habbahan, lemon grass, na’a na’a, girfa suna sha ko da sau daya a sati za ki iya saka tea bag ko wanne iri ne musamman masu qamshin dadi ga hoton wasu nan a qasa zan turo ba dole sai wannan ba makamantansu dai in kin je shagon akwai su, kuma ka da ki cika kayan shayin domin za su ce basa so amma in kika yi musu mai dadi za su rinqa miki tuni mama a dafa mana shayi sai ki saka musu sugar sosai 😋. Abubuwan da na ambata hulba ne mai daci a ciki kadan zaki rinqa zuba shi domin in yayi kamar magani ba za su sha ba. Sauran wadancan manyan herbs din ban saka su ba domin yara ne kuma ba su da infection din so zai kare su ya taimakawa jikinsu ne, duk wasu qananan ciwuka ba za su rinqa miki complain nasu ba in shaa Allah. 

Sannan na fadi juice mai kare jiki da kashe infections idan kin tashi yi abun da zaki hada musu shine danyen kurkum, lemun tsami, danyen citta, sai ki nemo foster clerks orange in kika niqe wadancan ko kika kankare sai ki tace ki zuba foster ki qara sugar yayi sanyi a fridge ko wa ya sha za su ma rinqa miki tuni a yi don da dadi😁. Kin ga cikin wayo da dabara kin magance musu matsaloli masu yawan gaske. 

Sannan kina kokarin sa su tsarki da ruwan dumi da gishiri in ma za ki iya ki rinqa dafa magarya da lalle ki zuba gishiri kadan su na tsarki da shi ko da sau daya ne a sati biyu, domin suna using toilet na school a can suke kwaso, ke ma toilet dinki na gida kina tsaftace shi tare da zuba gishiri. 

Haka nan panties dinsu a na wanke musu shi da ruwan dumi da gishiri in sha Allahu za su girma babu infection. 

Sannan kina communicating da su duk in sun ji zafi wurin futsari ko qaiqayi su fada miki sai ki yi maza ki musu abun tsarkin da nace amma ki sanya tafarnuwa wannan karon zai magance qaiqayin da jin zafin.

Sannan ki musu mixing man hulba, zaitun, da tafarnuwa sai ki shafe gabansu da yardan Allah za su girma babu shi in ma ya shiga zai rinka mutuwa. Wannan man sai in sun ce su na jin qaiqayi kuma yana barin musu qaiqayin sai ki a ajiye, a saman gabansu fa ban da can qasan. Har yayanki maza zasu iya tsarki da ruwan dumi da gishirin da tafarnuwa a koda yaushe.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending